Za a janye motoci sama da miliyan 3 a duniya

Taswirar kamfanin motoci na Toyota
Image caption Darajar hannayen jari na kamfanin Takata ya fadi da kashi tara cikin dari a kasuwar shunku na Tokyo

Kamfanonin kera motoci na Japan guda hudu za su janye motoci miliyan 3 da dubu 400 daga kasuwa, saboda jakar kariyar dake cikinsu na da matsala.

Kamfanin Toyota wanda zai janye motoci miliyan daya da dubu 73 ya ce, jakar kariyar dake bangaren fasinja na da matsala, ta yadda za ta iya fashewa ta cika da iska ta kumbara, ba ta yadda ya kamata ba a lokacin hatsari.

Haka kuma kamfanin kera motoci na Honda shi ma zai janye motoci miliyan daya da dubu 13 a fadin duniya.

Yayin da Nissan zai janye dubu 500, sai kuma Mazda wanda shi ma zai janye motoci dubu 45 a duniya.

Motocin da za a janyen, an sayar da su ne tsakanin shekarun 2000 zuwa 2004, kuma a cewar kamfanonin, kamfanin Takata ne ya samar musu da bangarorin motocin dake da matsala.

Manyan kamfanonin kera motoci na duniya dai sun sama janye motoci daga kasuwa, ko daga hannun wadanda suke amfani da su, da zarar sun gano cewa suna da matsaloli.