Amurka ta ce Korea ta Arewa ta mallaki makaman nukiliya

Harba makaman nukiliya a kasar Korea ta Arewa
Image caption Harba makaman nukiliya a kasar Korea ta Arewa

Wasu bayanan sirri na kasar Amurka sun ce kasar Korea ta Arewa ta mallaki wani makamin nukiliyar da zai iya tafiya tare da makamai masu linzami.

Sai dai binciken da cibiyar tattare bayan leken asiri ta ma'aikatar tsaron Amurkar ta gudanar ya ce, makaman nukiliyar basu da matabbaci.

Ta kuma ce ba daidai bane a hakikance cewa kasar Korea ta Arewar ta yi gwaji ko kuma kirkiri wadannan makamai.

A ranar Alhamis ne dai shugaban Barack Obama, yayi gargadin cewa Amurka da ta dauki duk wasu matakan da suka kamata na kare jama'arta da kawayenta daga kasar Korea ta Arewar dake barazanar daura damarar yaki.

Wata mata da ta yi gudun hijira daga kasar Korea ta Arewar zuwa Korea ta Kudu ta shaidawa BBC cewa mutanen Korea ta Arewar na bukatar yakin saboda abinda ta ce suna fatan cewar zai kawo karshen halin kuncin da suka shiga.

Tace mutane da yawa na shan bakar wahala a Korea ta Arewa, da ya suka gwammace cewa yakin shine abu mafi sauki da zai iya kawo karshen halin da suka haula'in da suka shiga.

Jami'an gwamnatin Amurkar ma dai na yin kira ga kasar China da ta yi amfani da tasirinta kan kasar Korea ta Arewar.