An kammala yakin neman zabe a Venezuela

Gangamin yakin neman zabe a kasar Venezuela
Image caption Gangamin yakin neman zabe a kasar Venezuela

A kasar Venezuela, an kammala gangamin yakin neman zaben shugaban kasa , wanda za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.

Zaben shugaban kasar zai maye gurbin marigayi shugaba Hugo Chavez, wanda ya mutu a cikin watan da ya gabata.

Dubban mutane ne dai sanye da jajayen riguna suka gudanar da wani gangami a kan titunan birnin Caracas, don nuna goyon bayansu ga mukaddashin shugaban kasar Nicolas Maduro, wanda ya dauki alkwarin ci gaba da aiwatar da manufofin Mr Chavez din.

Mr Maduro ya bayyana a kan dandamali tare da iyalan Mr Chavez da kuma shahararren dan wasan kwallon kafar nan na kasar Argentina, Diego Maradona.

A taron gangamin yakin neman zaben, Mr Maduro ya yi alkawarin ci gaba daga inda Mr Chavez ya tsaya.

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyar adawa, Henrique Capriles wanda ya fadi a zaben da suka fafata da Mr Chavez cikin watan Octoban bara, ya shaidawa dubban jama'ar da suka taru a jihar Apure cewa kasar Venuzuella na bukatar canji.