Champions League: An raba Real Madrid da Barcelona

real madrid
Image caption yan wasan kwallon kafa na Real Madrid da kuma Barcelona

Mai yiwuwa kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da kuma Real Madrid za su hadu a wasan karshe na gasar Champions League da za a yi a filin wasa na Wembley bayan da aka rabasu a wasannin gab-da na karshe.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Munich, yayinda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kara da Borussia Dortmund.

A ranar 23 da kuma 24 ga watan Afrilu za a buga wasannin, yayinda a ranar 30 ga watan Afrilu da kuma 1 ga watan Mayu kungiyoyin za su sake karawa da juna a zagaye na biyu.

A gasar zakarun turai kuwa, kungiyar kwallon kafa ta Chelsea za ta yi tattaki zuwa Switzerland a karawar zagayen farkon da za su yi da kungiyar kwallon kafa ta Basel a ranar ashirin ga watan Afrilu.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta kasar Turkiya Fenerbahce za ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Portugal watau Benfica yayinda zasu sake karawa zagaye na biyu a ranar biyu ga watan Mayu.

Chelsea ita kadai ce kungiyar kwallon kafa ta Birtaniya da ta rage a gasar zakarun Turai .