An dauki bakaken fata tamkar karnuka a Mumbai

Mr Sambo Davis da Matar shi
Image caption Mr Sambo Davis da Matar shi

'Yan Africar da ke zaune a ciki da kuma kewayen Mumbai, babban birnin harkokin kasuwanci na kasar India, suna korafi akan ana nuna musu banbancin launin fata.

Haka nan kuma sun yi zargin cewa 'yan sanda sun kafa musu karen tsana inda suke uzzura musu.

Babu dai wani adadi takaimaimai na yawan 'yan Africar da suke birnin Mumbai, to amma tun bayan ci gabar tattalin arzikin da India ta samu a' yan shekarun baya bayan nan, 'yan Africa da dama sun shiga birnin na Mumbai domin neman aiki a ciki kuma kewayensa.

Adadin da ba na gwamnati ba na cewa akwai 'yan Africa akalla dubu biyar.

Daga cikin wadannan 'yan africa, akwai 'yan Nigeria masu yawa, ya Allah masu karatu ne ko kuma masu gudanar da harkokin kasuwancinsu.

To saidai akwai daruruwan 'yan africa, akasarinsu kuma yan Nigeria wadanda basu da takardun izinin zama a kasar. Ko dai sun yar da fasfunansu ko kuma takardun izinin zamansu sun kare.

Wani dan Nigeria mai suna Mr Sambo Davis, wanda har ya auri wata 'yar Kasar India, yace banbancin da ake nuna masa ya kai intaha.

Yace saboda shi bakar fata ne ba'a iya bashi haya, sannan wasu lokuttan idan ya je cin abinci akan hana shi zama a wasu wurare da ake cewa an kebewa yan India.

Mr Sambo ya ce akwai lokacin da aka kamashi tare da wasu mutane talatin aka kulle, bisa zargin suna saida miyagun kwayoyi, amma gaskiya ta yi halinta a karshe, dole aka sake su aka basu hakuri.

To amma duk da haka sai gashi an wallafa a cikin jarida cewar an kama su ne saboda fasakwabrin miyagun kwayoyi. Yace abun da' yan sanda sun dauki bakar fata tamkar karnuka.

Saidai, Ahmed Javed, jami'in da ke kula da tabbatar da doka da oda, ya ce al'amarin ba haka ya ke ba, yace lamari ne da ya ke da rikir-kitarwa. Yace a lokutta da dama, wadannan 'yan Africa basu da takardun izinin zama sannan babu fasfo, kuma idan ba'a tabbatar da inda suka fito ba, ba za'a iya mayar da su kasashensu ba.