Al-Bashir ya kai ziyara Sudan ta Kudu

Al Bashir da Salva Kiir
Image caption Al Bashir da Salva Kiir

Shugaban Kasar Sudan Omar Al-Bashir ya kai ziyara zuwa kasar Sudan ta Kudu a karo na farko tun bayan da kasar ta samun 'yan cin kanta a cikin shekara ta 2011.

Shugaba Omar Al-Bashir da kuma takwaran aikinsa Salva Kiir, zasu tattauna akan batutuwan kan iyaka da na yankuna da suke takaddama akai.

Haka nan kuma akwai maganar yarjejjeniyar da kasashen biyu suka sawa hannu a kwanakin baya akan yawan kudin da Sudan ta Kudu zata biya Sudan saboda kyale ta tayi amfani da yankinta wajen jigilar mai zuwa bakin teku.

A bara, kasashen biyu sun kai gab da gwabza yaki akan sauran batutuwan da basu warware ba a tsakaninsu bayan da Sudan ta Kudu ta balle ta zama kasa mai cin gashin kanta.

To amma tun bayan da suka kulla yarjjeniya ta fitar da man Sudan ta Kudu, dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fara kyautata.

Karin bayani