Kasashe 6 na Tarayyar Turai sun amince kan biyan haraji

Babban Bankin Kungiyar Tarayyar Turai
Image caption Babban Bankin Kungiyar Tarayyar Turai

Kasashen shida da suka fi karfin tattalin arziki a tarayyar turai sun amince su hada kai wajen magance matsalar kin biyan haraji a kasashen su.

Kasashen sun bayyana cewa tarayyar turai na tafka dimbim asarar daya kai kimanin dala triliyon daya a kowace shekara saboda kin biyan harajin.

Ganawar da Ministocin kudi na kasashen shida suka yi a birnin Dublin, ta haifar da muhimman matakan da zasu kai ga cimma matsaya kan ceto wasu kasashen daga kangin tattalin arziki.

A karshen ganawar tasu, Ministocin kudi na kasashen shida sun amince da su baiwa kasashen Portugal da Ireland damar shekaru bakwai su gama biyan basssukan dake kansu, wanda ta hakan ne zai saukaka musu wajen tafiyar da harkokin kudaden kasashen nasu.

Ministocin dai sun gudanar da wani taron manema labaru na hadin guiwa ne a jiya juma'a, matakin da ake kallo a matsayin wani yunkuri na shawo kan kasar Austria ta sassauta dokokinta da suka shafi harkokin bankuna..

Kasar dai ita ce kasa ta karshe a tarayyar turai data ki amincewa hukumar tattara haraji a kasarta yin musayar bayanai da sauran kasashen dake nahiyar.

Ministocin sun kuma amince da manufofin tattalin arzikin Cyprus da aka tattauna tsakanin Tarayyar Turai da kuma jami'an Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF.

Hukumar Tarayyar Turai ta ce manyan kasashe mambobinta kamar su Birtaniya, Jamus da Faransa, na yin kiran da a rika samun musayar bayanai tsakanin hukumomin tattara kudaden haraji, wanda kasar Austria ke ci gaba da nuna turjiya a kai.