Amurka na neman sulhu a yankin Koriya

Johns Kerry a Koriya ta Kudu
Image caption Johns Kerry a Koriya ta Kudu

Kasashen Amurka da China sun ce sun kudiri aniyar aiki tare domin kawo karshen mafani da makaman nukiliya a yankin Korea.

Yayin wata tattaunawa da sakataren hulda da kasashen wajen Amurka, John Kerry, China ta yi kiran ayi amfani da tattaunawa wajen shawo kan rikicin yankin Korea.

Ministan hulda da kasashen wajen Chinan, Wang Yi yace, karuwar zaman dar-dar a yankin Korea ba zai zama alheri ga kowanne bangare ba.

China ta kuma yi kiran a kawo karshen gasar mallakar makaman nukiliya.

Wakiliyar BBC ta ce John Kerry yana matsala lamba ne ga Amurka tayi amfani da karfin fada-ajinta wajen hana Korea ta arewa ci gaba da yiwa Korea ta kudu da Amurka barazana.

Karin bayani