LSE ta zargi BBC da kin fadar gaskiya

Shirin Panorama na BBC
Image caption Shirin Panorama na BBC

Tawagar masu shirin Panorama na BBC sun dauki hotunan bidiyo a asirce na tsawon kwanaki takwas a watan da ya gabata, a wata tafiya da suka yi da wasu dalibai masu yawon bude ido, amma Jamiar nazarin harkokin tattalin arziki ta London wato London School of Economics ta yi amannar cewa fakaicewar da yan jaridun suka yi a matsayin dalibai sun saka tawagar cikin hadari.

Jamiar ta LSE ta zargi BBC da amfani da karya da kuma yaudara tun daga farkon tafiyar.

Ta ce bata da cikakken masaniya kan tafiyar, kuma BBC ta ki yarda ta dauki alhakkin jefa dalibansu cikin hadari.

BBC ta ce an sanarda daliban har sau biyu cewa wani dan jarida zai bi tawagar su kuma an yi musu gargadi kan yiwuwar kama su da kuma tsare su.

Amma dan jaridar John Sweeney ya shaida cewar ba a gaya musu cewa akwai wasu a tawagar su uku da suke daukar hotunan bidiyo ba na zahirin al'amurran dake gudana a asirce don yin wani shiri mai mahimmancin gaske ba.

Karin bayani