Tarzoma a kurkukun Guantanamo

Kurkukun tsibirin Guantanamo
Image caption Kurkukun tsibirin Guantanamo

Wasu masu gadin kurkukun soji na tsibirin Guantanamo sun yi ta harbe- harbe da harsashen roba don kwantar da tarzomar da ta barke a gidan kurkukun.

Tarzomar ta abku ne lokacin da ake kokarin maida fursunonin dakunan da ake tsare dasu.

Jami'ai a gidan kurkukun na gwamnatin Amurka dake Cuba sun ce wasu fursunoni ne suka yi amfani da wasu makamai da suka harhada don hana komawa dasu cikin dakunansu.

Zaman dar-dar ya karu a gidan kurkukun sakamakon yajin kin cin abinci da wasu fursunonin suka fara tun a watan Fabrairu, bayan da wasu fursunoni suka zargi masu gadinsu da bincika Kur'anan da suke amfani dasu kan ko suna dauke da wasu abubuwa da aka haramta.

Jami'an gidan kurkukun na Guantanamo sun ce fursuna guda ne kawai ya samu raunuka lokacin tarzomar..

Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da lauyoyi sun ce, wannan na faruwa ne sakamakon gazawar da hukumomin suka yi wajen yanke shawarar yadda za su tafiyar da fursunonin, da akasarin su sun shafe fiye da shekaru goma.

Bayanai dai sun ce Jami'an gwamnatin Amurka sun riga sun bada umarnin a saki kimanin casa'in daga cikin fursunonin, amma kuma har yanzu ana ci gaba da rike.

Wannan kuwa na faruwa ne sakamakon wasu dalilai da suka shafi ka'idojin fitar dasu daga gidan kurkukun, da kuma tunanin yiwuwar musguna musu bayan an maishe su kasashen su.