Akalla farar hula 27 ne aka kashe a Somalia

Al- Shabaab ta kai hare-hare
Image caption Al- Shabaab ta kai hare-hare

Kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Al Shabaab ta kaddamar da hari mafi muni a Mogadishu, baban birnin Somalia tun bayan an fatattake su daga birnin a watan Agustan shekarta ta 2011.

'Yan kungiyar Al Shabaab din su tara ne suka auka cikin kotu mafi girma a birnin dauke da muggan makamai inda suka hallaka mutane da dama.

An dai yi ta musayar wuta kuma wani ministan gwamnati yace, an kashe dukkan 'yan bindigar.

Sai dai kuma kungiyar Al Shabaab tace, mambobinta da suka yiwa kansu sulke da bam shida ne kawai aka kashe a lokacin fafatawar.

A dayan kuma harin kunar bakin wake ne aka kai kan ayarin motocin ma'aikatan agaji na kasar Turkiya dake kan hanyar zuwa filin jiragen saman birnin.

Karin bayani