Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Venezuela

Zaben shugaban kasa a Venezuela
Image caption Zaben shugaban kasa a Venezuela

Yayinda 'yan sa'oi suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa a Venezuela, dan takara a jam'iyar adawa, Henrique Caprilles ya zargi shugaban Nicolas Maduro da sabawa dokokin zabe.

Shugaban rikon kwarya, Nicolas Maduro, wanda marigayi shugaba Hugo Chavez ya zaba a matsayin wanda zai gaje shi, zai fafata ne da Jagoran adawa, Henrique Caprilles.

Mr Caprilles dai ya fadi a zaben da suka fafata da marigayi Mr Chavez a zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin watan Oktobar bara.

A taron manema labaran, Mr Caprilles ya nanata zargin da yake yiwa Mr Maduro, yana cewa ya sabawa ka'idojin zabe, ta hanyar bayyana a kafar talabijin ta kasar, bayan da aka dakatar da yakin neman zabe.

Mr Maduro dai ya gudanar da jawabai a gidan talabijin na kasar, lokacin da ya kai ziyara makwancin Mr Hugo Chavez.

Ziyarar makwancin Mr Chavez

Ziyarar dai ta kasance daidai da zagayowar cika shekaru 11 da dawowa kan karagar mulkin da Mr Chavez ya yi, bayan wani dan gajeren juyin mulki.

Mr Maduro, ya yi kira ne ga 'yan kasar Venezuela da su tuna da kamalar Mr Chavez a lokacin da suka je kada kuri'a.

A lokaci guda kuma, abokin karawar ta sa Mr Caprilles shima ya yi kira ga masu kada kuri'ar da su zabi gaskiya bisa karya.

Mr Maduro dai shine na kan gaba-gaba a zaben, amma kuma kuri'un jin ra'ayoyin jama'a na baya bayan nan sun nuna cewa ratar da ke tsakanin 'yan takarar biyu na kara tsukewa.

A ranar 19 ga watan Aprilu ne za a rantsar da duk wanda ya samu galabar lashe zaben, kana sabon shugaban kasar zai gudanar da mulki har ya zuwa shekara ta 2019, domin karasa shekaru shidan da ya kamata Mr Chavez ya fara tun daga watan Janairu.