Shugaban Iran ya fara ziyara a Nijar

Mahmud Ahmedinejad
Image caption Shugaban Iran

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmedinejad ya fara wata ziyara a jamhuriyar Nijar. A lokacin ziyarar, Shugaba Ahmedinejad zai gana da shugaba Mahamadou Issoufou na jamhuriyar Nijar domin shawarwari.

Shugaban na Iran ya isa jamhuriyar Nijar ne daga Benin, zangon sa na farko a ziyarar da ya shirya zuwa kasashe uku na Afrika.

A wani jawabi da yayi a Benin, Shugbaa Mahmud Ahmedinejad, ya kare shirin nukiliyar Iran da ake cece-kuce akansa, ya na mai cewar Iran ba ta da wata bukata ta kera bomb na nukiliya.

Shawarwarin na Shugaba Ahmedinejad a Benin sun maida hankali akan harkokin noma da makamashi da kuma ilimi.

Iran ta na bukatar karfen Uranium saboda shirinta na nukiliya, Nijar kuma ita ce kasa ta hudu a duniya mai arzikin karfen Uranium.

A 'yan watannin baya, Nijar ta soki lamirin yarjjeniyar da ta dade ta na amfani da ita tsakaninta da Faransa akan batun Uranium.

Karin bayani