Najeriya ta kafa kwamitin sasantawa da Boko Haram

Daya daga cikin Hare-Haren Boko Haram
Image caption Daya daga cikin Hare-Haren Boko Haram

Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da kafa wani kwamiti da zai sasanta da kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus Sunna Lid da'awati wal Jihad da ake fi sani da suna Boko Haram.

Hakan ya biyo bayan nazarin da Majalisar tsaron Nijeriya ta yi ne akan wani rahoto da aka gabatarwa shugaban akan batun yiwa 'yan kungiyar ta Boko Haram afuwa.

Makwanni biyu da suka wuce ne dai, Shugaban Nijeriyar ya dorawa wasu jami'an tsaron kasar alhakin duba hanyoyin da za'a bullowa al'amarin tsaro na kasar.

Kwamitin dai yana karkashin jagorancin ministan ma'aikatar ayyuka ta musaman na kasar ne Malam Kabiru Tanimu Turaki.

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Goodluck Jonathan ya nada kwamitin ne bayan da majalisar koli kan tsaro ta yi nazari kan rahoton da wani kwamitin wucin gadi ya bayar akan hanyoyin da za'a bi domin shawo kan matsalar tsaro a arewacin kasar.

Mambobi ashirin da shida

Gwamnatin kasar ta ce an dorawa kwamitin alhakin tattaunawa da shugabanin kungiyar Jama'atu Ahlus Sunna Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da suna Boko Haram game da afuwar da gwamnatin kasar ke shirin yi musu tare kuma da samar da hanyoyin da za'a bi domin warware tashe- tashen hankulan da ake fuskanta a kasar .

Kakakin shugaban kasar Reuben Abati yayi wa manema labarai karin bayani.

"Ayyukan da kwamitin zai yi sun hada da fito da tsare-tsaren da za a bi wajen yin afuwar, da kuma samar da tsare-tsare tsaren da za'a bi ta yadda 'ya'yan kungiyar za su ajiye makamansu nan da kwanaki sittin. Da kuma samar da shawawari akan yadda za'a taimakawa mutanen da lamarin ya shafa da kuma matakan da za'a dauka domin shawo kan abubuwan da ke janyo tada kayar baya."

Wakilan kwamitin dai sun hada da Malaman addini Kamar Sheikh Ahmed Lemu da Dr Ahmed Datti da Malam Salihu Abubakar, da tsaffin Jami'an gwamnati Kamar Dr Hakeem Baba Ahmed da Ambassador Zakari Ibrahim da kuma wasu fitattun 'yan Nigeria kamar Professor Nur Alkali da ma masu fafutukar kare hakkin Jama'a.

Fadar shugban kasar ta ce shugaba Goodluck Jonathan ya nada wani kwamiti da aka dorawa alhakin yin nazari akan yaduwar kananan makamai a kasar, karkashin jagorancin Ambasada Emmaneul Imohe.

Ta ce shugaban kasar ya dau matakin ne domin cika alkawarin da ya yi akan cewa Najeriya za ta yi aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen duniya domin magance matsalar yaduwar kananan makamai da ake amfani dasu wajen tada husuma a cikin kasar da kuma wasu kasashe masu tasowa.

Sunayen 'yan kwamitin sasantawa da Boko Haram

1. Kabiru Tanimu Turaki, Ministan ayyuka na musamman - Shugaba

2. Sheik Ahmed Lemu - Wakili

3. Dr. Hakeem Baba Ahmed - Wakili

4. Col. Musa Shehu, (rtd.) - Wakili

5. Sheik Abubakar Tureta - Wakili

6. Dr.Datti Ahmed - Wakili

7. Senator Sodangi Abubakar - Wakili

8. Senator Ahmed Makarfi - Wakili

9. Hon. Mohammed Bello Matawalle - Wakili

10. Amb. Zakari Ibrahim - Wakili

11. Comrade Shehu Sani - Wakili

12. Hajiya Naja’atu Mohammed - Wakili

13. Malam Adamu S. Ladan - Wakili

14. Dr. Joseph Golwa - Wakili

15. AVM A. I. Shehu - Wakili

Image caption Illar hare-haren Boko Haram

16. Mr. R. I. Nkemdirim - Wakili

17. DIG P. I. Leha - Wakili

18. Prof. Nur Alkali - Wakili

19. Malam Salihu Abubakar - Wakili

20. Alhaji Abubakar Sani Lugga - Wakili

21. Barrister Ibrahim Tahir - Wakili

22. Brig-Gen. Ibrahim Sabo - Wakili

23. Amb. Baba Ahmed Jidda - Wakili

24. Group Capt. Bilal Bulama, rtd. - Wakili

25. Prof. Bolaji Akinyemi - Wakili

26. Wakilin ofishin sakataren gwamnatin tarayya - Sakatare