An kama Karim Wade a Senegal

Karim Wade
Image caption Ana zargin Mr Wade da tara makudan kudade ta haramtacciyar hanya

'Yan sanda a Senegal sun kama Karim Wade, dan tsohon shugaban kasar, Abdoulaye Wade, bisa zargin tara makudan kudade ta haramtacciyar hanya,da yawansu ya kai dala biliyan daya da miliyan dari hudu, a zamanin mulkin mahaifinsa na tsawon shekaru sha biyu.

Karim Wade ya kasance na hannun daman mahaifin nasa a zamanin mulkin, inda aka rika kashe makudan kudade kan kwangilar ayyukan more rayuwa.

A lokaci guda ya rike mukamin ministan ayyuka, da kyautata hulda da kasashe, da na makamashi, da kuma na sufurin jiragen sama, wadanda in aka hada kasafin kudinsu, ya kai kwatankwacin kashi daya cikin uku na daukacin kudaden da gwamanati ke kashewa.

Wata kotu ta tsayar da wa'adin yau Litinin, ga Karim Wade da ya bada hujjojin da zasu wanke shi daga zargi.