FBI ta ce tana bincike kan harin Boston

Image caption Hukumar FBI na bincike kan tashin bam a Boston

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka wato FBI ta ce ta na gudanar da abinda ta kira kwarya-kwaryar binciken ta'addanci kan abubuwa biyun da suka fashe a Boston.

Akalla mutane 3 ne suka mutu wasu da dama kuma suka sami raunuka, a fashewar wasu abubuwa a daidai layin da ake kammala tseren gudun yada-kanin-wani na Boston a Amurka.

Har wa yau akwai wutar da ta tashi a kusa da dakin bincike da nazarin littatafai na Boston din.

Hukumar 'yan sandan Boston ce ta tabbatar da mutuwar mutanen a yayinda ta ce akwai daruruwa dake dauke da munanan raunuka.

Shugaban Amurka Barack Obama, a wani jawabi da ya yiwa al'ummar kasar, ya ce su kwantar da hankalinsu a yayinda gwamnati take yin duk abinda za ta yi domin gano wadanda su ka tayar da bama baman.

Mista Obama ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma jajantawa al'umar garin Boston.

Wasu hotuna da ake nunawa kai tsaye daga wurin da lamarin ya faru, sun nuna mutane jina-jina, ma'aikatan kiwon lafiya na yi musu magani.

Motocin daukar marasa lafiya masu yawa da na 'yan sanda da kuma na jami'an kashe gobara sun isa wurin, domin bada agaji.

Wani dalibi mazaunin garin ya shaidawa BBC Hausa cewa, jama'a da dama na cikin kaduwa a garin na Boston.

Ya ce ya zuwa yanzu an dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa da na bas a yayinda aka tsananta bincike a garin.

Image caption Taswirar Harin Boston

Idan dai wannan harin aka tabbatar na ta'addanci ne zai iya zama hari mafi muni da aka yi a tsakiyar birni a Amurka tun harin da aka kai na 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001.

Karin bayani