Afrika ta Tsakiya ta nemi taimakon Faransa

Dakarun Seleka a Bangui
Image caption Har yanzu ana zaman zullumi a Bangui

Pirayi Ministan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Nicolas Tiangaye, ya bukaci taimakon Faransa da wasu makwabtan kasar don samar da tsaron a cikin kasarsa.

A yammacin ranar Talata ne, wasu tsageru suka kashe tsaffin dakarun 'yan tawaye bakwai a babban birnin kasar, Bangui.

Har yanzu ana zaman zullumi a Bangui tun bayan da 'yan tawaye suka kifar da gwamnati a watan da ya gabata.

A gobe Alhamis ne, shugabannin yankin za su tattauna a kasar Chadi don yin mahawara a kan bukatar da gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta gabatar, na a tura ma ta karin dakarun samar da zaman lafiya a cikin kasar.