An yi Jana'izar Margaret Thatcher

Sarauniyar Ingila a wajen Jana'izar Margret Thatcher
Image caption Sarauniyar Ingila a wajen Jana'izar Margret Thatcher

Babban bishop na birnin London ya ce tsohuwar Fira ministar Burtaniya Baroness Thatcher ta huta "bayan rayuwar siyasa mai cike da cece-kuce", kamar yadda ya fada a lokacin jana'izarta.

Right Reverend Richard Chartres ya jinjina wa halayyar ta, da yadda ta taso da irin kulawar da take nuna wa ga sauran mutane.

Fira ministan Burtaniya David Cameron ya bayyana jana'izar da cewa "wata girmamawa ce ga gwarzuwar Fira minista".

Sarauniyar Ingila Elizabeth na daga cikin manyan baki 2,000 da suka halarci jana'izar.

'yan sanda dubu hudu ne suka yi aikin tabbatar da tsaro a tsakiyar birnin Landan, yayinda dimbin mutane suke jeru a kan hanyoyin da aka wuce da gawar ta, wadda aka girmama da bukukuwan soji.

Akwai rahotannin da ke cewa an samu wasu mutane da suka gudanar da zanga-zanga, sai dai Right Reverend Chartres ya shaida wa wadanda suka taru a cocin St Paul cewa, "yau ba rana ce ko lokacin da za a yi tattaunawar siyasa game da mamaciyar ba".

Karin bayani