An gano wanda ake zargi da hare haren Boston

Masu binciken harin da aka kai Boston
Image caption Masu binciken harin da aka kai Boston

Rahotannin kafofin watsa labarai a Amurka sunce masu bincike sun sun gano wanda ake zargi da kai harin Bam a lokacin gudun fanfalaki a Boston daga wani hoton Bidiyo.

Rahotannin sunce hukumomi suna da hoton wanda suke zargin yana dauke da wata jikka a daya daga wuraren da aka dana bam din.

Yansandan Boston sun musanta rahotannin cewar an yi kame dangane da al'amarin.

Nan ba da jimawa ba ake sa ran wata sanarwar hukuma da ta fito daga hukumar bincike ta Tarayya -- FBI.

Mutane uku ne suka mutu sannan wasu fiye da 170 suka jikkata lokacin harin.

A waje daya kuma,Hukumar bincike ta tarayya a Amurka wato FBI ta ce gwajin farko da aka gudanar na nuna cewar wata wasika da aka aikewa shugaba Obama na kunshe da sinadari mai guba- mai suna RICIN.

Amma a cewar hukumar ta FBI babu alamun dake nuna cewar wasikar nada alaka da hare-haren bam din na Boston.