Jam'iyyar ACN za ta gudanar da babban gangami a Lagas

A yau ne babbar jam'iyyar adawa ta Action Congress of Nigeria zata gudanar da babban gangamin a jihar Lagos don amincewa da kafa wata babbar jam'iyya da sauran jam'iyyun adawa a shirin da suke, na karbe mulki daga jam'iyyar PDP a shekara ta 2015.

Sai dai babban taron na jam'iyyar ACN a yau, zai ci karo da wata ziyara da shugaban Naijeriya Dr. Goodluck Jonathan zaiyi a Lagos.

Wannan dai shine wani gangami da jam'iyyar Action Congress of Naijeriya ta kira wadda ba kawai taro ne na kuwwa da furta kalaman siyasa ba.

A'a taro ne na neman yaddar 'ya'yan jam'iyyar ACN a daukacin fadin Naijeriya dan daukar matsayin kafa babbar jam'iyya da sauran jam'iyyyun adawa a kasar.

Wadda a shekara ta 2015 suke da aniyar karbe ragamar shugabancin kasar daga jam'iyyar PDP mai mulki.

Sai dai taron na jam'iyyar ACN yazo a daidai lokacin da shugaban Naijeriya Dr. Goodluck Jonathan zai kawo wata ziyara Lagos.

Wani abu da jam'iyyar ACN ke cewa hakan zai iya haifarwa a toshe hanyoyi dan shugaban kasa ya wuce wadda hakan zai iya hana membobin jam'iyya ACN isa wajen taron.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak ya ce ziyarar shugaban kasa Lagas ba zai shafi gangamin na jam'iyyar ACN ba.

Gwamnonin jam'iyyar ACN da CPC da ANPP da kuma wani bangaren jam'iyyar APGA sun amince su kafa jam'iyya daya dan karbe mulki daga jam'iyyar PDP mai mulki a shekara ta 2015.

Anan gaba ne dai sauran jam'iyyun za su gudanar da irin wannnan gangami wadda daga bisani za ayi gagarumin gangamin sanarwa hadewar jam'iyyu a wata babbar farfajiya da ba a bayyana ba.