Za'a tura karin sojoji janhuriyar Afurka ta tsakiya

Image caption Shugababannin jamhuriyar Afurka ta tsakiya

Kasashen yankin tsakiyar Afrika sun yi alkawarin kara karfin rundunar kiyaye zaman lafiyar da suka tura jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da dakaru dubu biyu.

Sun dauki matakin ne a karshen taron da suka gudanar a Ndjamena, babban birnin kasar Chadi.Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta kara shiga rudani ne bayan da a watan jiya 'yan tawaye suka kwace iko.

Sojojin Afrika ta Kudu goma sha uku ne suka mutu a artabu da 'yan tawaye a cikin watan da ya wuce.

Tun daga nan ne kuma jamhuriyar tsakiyar Afrika take cikin rikici da rashin zaman lafiya.

Yanzu haka dai ma'aikatan kasar na cikin wani hali saboda rashin biyansu albashi.