Jama'a sun kashe wasu 'yan bindiga a Kano

Image caption Jihar Kano dai na fama da hare-haren kungiyar 'yan Boko Haram

Wasu da ake zargi yan bindiga ne su biyu sun rasa ran su bayan jefa wani abun fashewa a kusa da katangar gidan fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Rahotanni sun ce maharan dai sun je ne a babur mai kafa uku da ake kira adaidaita Sahu, inda suka jefa abin da suke dauke da shi.

Sai dai jama'a sun kama su, inda daya ya mutu nan take dayan kuma ya mutu bayan jami'an tsaro sun tafi da shi.

A cewar wadanda abun ya faru a kan idanunsu, maharan sun je kofar arewa wadda aka fi sani da kofar fatalwa ta fadar mai martaba sarkin Kano da Misalin karfe 8.30 na dare.

Su ka jefa abun da suke dauke da shi wanda ya fashe tare da kara da ta firgita mutanen wajen. Jefa abun ke da wuya mutanen su ka yi kokarin tserewa, inda jama'a su ka bisu su ka kama su.

Shaidu sun tabbatar da cewa a nan take daya daga cikin maharan ya rasa ransa bayan dukan kawo-wuka da jama'a su ka yi masa.

Sannan aka kona babur din da su ka je da shi yayin da aka mika dayan ga jami'an tsaro.

Kakakin rudunar tsaro ta JTF da ya tabbatar da lamarin ya ce wanda aka mika musu dinma ya rasu.