Bindigogi- Obama ya soki Majalisar Amurka

Shugaba Obama ya soki Majalisar dattawan Amurka saboda fatali da suka yi da wani kuduri wanda zai sa a yi zurfin bincike kafin a siyarwa mutane bindiga a kasar.

Image caption Shugaba Obama ya ce yan Majalisar sun yi abun kunya

Shugaban kasar ya bayyana matakin da Majalisar ta dauka a matsayin abun kunya a Washington

Mista Obama dai ya sha alwashin ci gaba da ganin a tsaurara dokokin mallakar bindiga tun bayan wani hari da aka kaddamar a makarantar Newton a watan Disambar shekarar bara.

'Yan uwan yaran da aka kashe a Newtown sun halarci zaman majalisar dattijai domin ganin yadda za'a kada kuri'a.

'Yan uwan yaran da kuma Jami'ai a White House dai sun yi fatan cewa majalisar za ta yi la'akari da ta'adin da aka yi a Jihar Connecticut na bindige yaran da basu ji ba basu gani ba a matsayin matashiya na tsaura dokokin mallakar bindigo a Amurka.

Kudirin da zai sa ayi zurfin bincike a kan masu siyan bindiga bai samu goyon bayan yan majalisar ba, inda ake bukatar kuri'un yan majalisa sittin cikin dari kafin ya samu amincewar Majalisar.

Sai dai yan Jam'iyyar Republican arba'in da daya da kuma 'yan Demokrat biyar ne su kada kuri'ar kin amincewa da kudurin duk da kamun kafan da shugaba Obama ya yi ta yi game da kudurin.

Da ya ke Jawabi bayan zaman majalisar, Shugaba Obama ya ce yan majalisar sun fuskanci matsin lamba ne daga dillalan bindigogi abun da kuma yasa suka bada kai bori ya hau.

Ya ce; "ina so a shaidawa al'ummar Amurka cewa, har yanzu zamu iya kawu sauyi da zai rage irin tashe-tashe hankulan da ake yi da bindigogi, idan har dai al'ummar kasar basuyi kasa a gwiwa ba. "

Shugaban Obama ya ce ba zai yi kasa a gwiwa domin zai ci gaba da fafutukar ganin a tsaurara dokokin mallakar makamai a kasar.

Matakin da Majalisar ta dauka dai ya zama babban koma baya a siyasance ga gwamnatin sa. Watannin hudu bayan harbin da aka yi a garin Newtown, har yanzu dai kasar Amurka ta gagara tsaurara dokokin mallakar bindigogi.