Texas: Mutane 15 sun mutu

Image caption 'Yan kwana-kwana sun kai ɗauki

'Yan sanda a jihar Texas ta Amurka sun ce, wani abu mai ƙarfin gaske da ya fashe a wani kamfanin yin takin zamani ya kashe mutane goma sha biyar, kuma ya jikkata wasu mutanen fiye da ɗari da sittin.

Gobara ta tashi a masana'antar yin takin zamanin jiya da maraice.

'Yan kwana-kwana sun shiga masana'antar suna ƙoƙarin kashe wutar, kwatsam sai aka ji wata fashewa mai ƙarfi da misalin ƙarfe takwas na dare agogon yankin.

Wani mutum shi da 'yar sa da suke kusa da wajen a lokacin sun ga lokacin da fashewar ta auku, kuma ƙarar ta girgiza su.

Masana'antar tana wani ƙaramin gari ne da ke gabashin Texas, kuma akwai shaguna da gidajen zaman jama'a a kusa da ita.