Mutane da dama sun mutu a gobarar Texas

Image caption Wani abu ya fashe a Kamfanin taki a Texas

Wani abu da ya fashe saboda wutar da ta kama a wani Kamfanin taki a jihar Texas dake Amurka ya halaka tsakanin mutane biyar zuwa goma sha biyar ya kuma jikkata sama da mutane dari da sittin.

Magajin wani karamin gari a Yammaci ( Tommy Muska) ya kwatanta fashewar abun da tashin nukiliya wanda ya ke tada hazo.

'Yan sanda sun ce hayakin da abun da ya fashe ya jawo ba zai zama barazana ga al'umma ba.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan yankin ya ce suna kallon wajan da abun ya fashe a matsayin wani wurin da aka aikata laifi, ko da yake ya ce ba bu wata alama da take nuna cewa anyi aika-aika a wurin.

Ya ce ana ci gaba da ayyukan ceto har sai sun kammala binciken gida-gida a gidajen da ke makwabtaka da Kamfanin sarrafa takin.

Karin bayani