Amurka na cikin juyayi

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama ya yaba ma al'ummar Boston, a lokacin wani taron addu'o'i ga wadanda hare haren bam da aka kai a birnin ranar Litinin ya rutsa da su.

A lokacin taron addu'o'in na hadin gwiwa tsakanin mabiya addinai daban daban, Mr Obama ya ce bama-bamai ba zasu karya zukatan mazauna garin na Boston, ko ma Amurka baki daya ba.

Haka nan masu gabatar da kara a Amurkar, sun tuhumi wani mutum da laifin aika wasikar da aka yi amannar cewa tana dauke da gubar nan mai hadari ta ricin, ga shugaba Obama.

Can kuma a jihar Texas ta Amurkar ana can ana ci gaba da ayyukan ceto da na agaji, bayan wata mummunar gobara da ta tashi a wata masana'antar yin takin takin zamani, inda ta halaka mutane sha biyar, wasu daruruwa suka jikkata.