Bam ya hallaka mutane 20 a Iraqi

Image caption An dana bam din ne a wani wurin shan shayi

'Yan sanda a Bagadaza babban birnin kasar Iraqi, sun ce akalla mutane ashirin da bakwai ne suka rasa rayukan su, a wani tashin bam da ya afku a yammacin birnin.

Wani dan kunar bakin wake ne ya dana bam a cikin wani shagon shan shayi a yammacin jiya a unguwar Amriyah wadda yawanci 'yan sunni ne ke zaune a cikinta.

Akalla akwai yara biyu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu, yayinda da dama kuma suka samu raunuka.

Shagon da aka dana bam din dai na cike da matasa ne, inda suke shakatawa.