Boston: an cafke Dzhokar Tsarnaev

Image caption Dzhokar Tsarnaev, yana hannun jami'an tsaro

'Yan sanda a birnin Boston na Amurka, sun cafke mutum na biyu da ake zargi da kai harin bom a tseren famfalaki da aka yi a birnin ranar Litinin.

'Yan sandan sun sami wanda ake zargin mai suna Dzhokhar Tsarnaev a ɓoye a cikin wani kwale-kwalen da aka ajiye a bayan wani gida.

Wani mutum ne dai ya bi diddigin digon jinin wanda ake zargin ne ya tsegunta wa 'yansandan.

An dai cafke wanda ake zargin, Dzhokhar Tsarnaev, mai kimanin shekaru 19 da haihuwa dan kabilar Chechen ne bayan wata musayar wuta.

Yanzu haka ana yi masa magani a asibiti sakamakon raunukan da ya samu.

A shekaru goman da suka gabata ne dai suka baro Dagestan dake gabashin Checheniya, zuwa Amurka shi da yayansa Tamerlan, wanda 'yansanda suka hallaka a wata musayar wuta.

Mahaifinsu wanda a yanzu haka yana zaune ne a Dagestan din ya ce an yiwa 'yayansa kage ne.

Amma kuma kawunsu wanda ke zaune a Amurka ya shaidawa gidan talabijin na kasar cewa, 'yayan dan uwan nasa sun bar abin kunya ga iyalansu, dama 'yan kasar Checheniya.

Wata gwaggon wadanda ake zargin dake birnin Toronto ta ce bata yarda cewa suna da hannu a kai harin na ranar Litinin ba.

Harin bom din na ranar Litinin a birnin Boston,dai ya yi sandiyyar mutuwar mutane uku tare da jikkata fiye da dari da saba'in.