Dzhokar Tsarnaev na kwance a asibiti

Dzhokar da Tamerlan
Image caption Maharan Boston

Jami'ai a Amurka sun ce wani kwamiti na masu bincike na musamman na jiran yiwa mutumin dayan da ya yi saura wanda ake zargi da kai harin bam lokacin gudun ya da kanin wani da a kai a birnin Boston.

Ranar juma'a da daddara ne aka kama Jokhar Sanayev mai shekaru 19 da haihuwa wanda dan asalin Chechenya ne a daya daga cikin gagarumar farautar da aka ta ba yi a tarihin 'yan sandan Amurka.

Jokhar Sanayev dai ya samu raunuka na harsasai da dama a musayar wutar da aka yi.

Kuma an ce ya na cikin wani mummunan hali amma ba mai hadari ba, a wani asibiti da aka sawa tsatstsauran tsaro.

Kwana daya kafin kama Jokhar Sanayev, an kashe yayansa, Tamerlan, a wata musayar wuta, wanda shi ne mutum na biyu da hukumar gudanar da bincike ta Amurka FBI ke zargi da hannu a hare haran bama-baman na Boston.

Masu gudanar da bincike na tarayya sun tabbatar da cewa shekaru 2n da suka wuce sun yi maga da Tamerlan akan daukar tsatstsauran ra'ayi bayan da wata kasa ta nemi ta yi hakan. Har ila yau an gano cewa bara ya yi wata shida a Rasha.

A jawabinsa na mako-mako, shugaba Obama ya yabawa dubban jami'ai na tarayya da kuma 'yan sandan da sukaI aikin nemo maharan---- dama jama'ar Boston baki daya.

Karin bayani