China: girgizar ƙasa ta kashe mutane 150

Image caption Ma'aikatan agaji

Wata kafar yaɗa labaran ƙasar China ta ce, sama da mutane ɗari da hamsin ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wata mummunar girgizar ƙasa da ta yi kaca-kaca yankin Chengdu dake yammacin ƙasar.

Da misalin ƙarfe takwas na safiya lokacin yankin ne mutanen yankin Sichuan suka wayi gari da jin kara mai ƙarfin gaske.

Girgizar ƙasar dai kusan ta sha shafi komai a yankin.

Ma'aikatan bada agaji suna ta kokarin bayan zaftarewar ƙasa ta katse tituna, kuma ya hana ma'aikatan agaji kaiwa gawasu ƙauyuka da dama da lamarin ya shafa.

Rahotanni dai na cewa, gine-gine da dama ne suka rushe a yankin.

Tuni dai aka aika dubban soja da 'yan sanda zuwa yankin domin bada agajin gaggawa.

Gidan talabijin na gwamnati ya nuna ana zaƙulo mutane da rai daga cikin gine-ginen da suka rushe.

Primiyan Chinan, Li Keqiang ya isa lardin da lamarin ya auku.

Lardin Sichuan dama ya sha fama da girgizar ƙasa.

A watan gobe ne dai za'a tuna cika shekaru biyar da aukuwar girgizar kasar da ta hallaka mutane kusan dubu casa'in a wannan yankin.