An fara gudanar da zaben a kasar a Iraqi

Zabe a kasar Iraqi
Image caption Zabe a kasar Iraqi

A yau ne al'ummar kasar Iraqi suka fara kada kuri'unsu a wani zaben da zai zamo zakaran gwajin-dafi na dorewar harkokin mulkin kasar.

Zaben ya biyo bayan hambarar da marigayi Shugaba Saddam Hussein shekaru goma da suka gabata.

Fiye da shekara guda kenan tun bayan rukunin karshe na sojojin Amurka sun fice daga kasar, inda a karon farko jami'an tsaron kasar ta Iraqi ne za su sa ido ga zaben.

Za a gudanar da zaben ne sha biyu daga cikin gundumomi sha takwas na Iraqi.

An kara samun barkewar tashe-tashen hankula gabanin zaben gundumomi.

Baya ga karuwar barkewar tashe-tashen hankula, an kashe 'yan takara a kalla goma sha uku wadanda suka yi niyyar shiga zaben.

'Yan takara fiye da dubu takwas ne za su yi takarar neman kujerun kansiloli, kana mutanen da suka cancanci kada kuri'a sun zarce miliyan goma sha uku.