Dzhokhar da Tamerlan sun shirya kai wasu karin hare hare- 'Yan sanda

Edward Davis
Image caption Mr Davis ya ce akwai hujjojin dake nuna cewa wadanda ake zargin sun shirya kai wasu hare-haren

Kwamishinan 'yan sanda na Boston dake jihar Masassuchets a Amurka, ya ce ya yi amannar cewa mutanen nan biyu da ake zargi da kai harin bam a lokacin gudun yada kanen wani da aka yi a birnin, sun shirya kai wasu karin hare-haren.

Kwamishina Edward Davis ya fadawa gidan talabijin na CBS cewa 'yan uwan junan biyu da ake zargin, suna da isassun nakiyoyin da ba su fashe ba da kuma bindigogi don kai hari a wasu wuraren dabam.

Mr Davis ya ce hujjojin da suka samu a wurin da aka kai harin, sun nuna cewa mutanen sun shirya kai hari a kan wasu karin mutane.

An dai kashe daya daga kicin mutanan da ake zargin, wato Tamerlan Tsernaev, a wata musayar wuta da 'yan sanda a lokacin da ake farautarsu, lamarin da ya kare da kama dayan, Dzhokhar.

Yanzu haka dai yana kwance a wani asibiti a Boston din, inda aka ce yana cikin matsanancin hali.

A halin da ake ciki kuma, dangin mutanen biyu da ake zargi, sun ce babban dan uwan, watau Tamerlan, bai da ra'ayin kyamar Amurka, amma a lokacin da ya ziyarci Dagestan a bara inda ya shafe watanni 6, sun gaano cewa ya samu tsattsauran ra'ayin Isalama ne a lokacin da yake zaune a Amirka.

Hukumomi dai na fatan cewa idan suka yi ma Dzhokhar din tambayoyi, za su samu karin haske a kan ainhin dalilan da suka sa aka kai harin, amma wasu rahotanni na nuna cewa ba zai iya taba magana ba saboda munanan raunika da ya samu.

Karin bayani