Mata a India na fargaba

Praminstan India, Manmohan Singh, ya ce kasar sa ta samu gagarumin ci gaba wajan kare mata kuma alhakin kowane dan kasa ne ya samarwa matan tsaro.

Har ila yau ya yi kiran da a rika yin takatsantan wajan kwantarwa da mutane hankali.

Kalaman nasa dai sun biyo bayan zanga zanar da akkai ta yi ne ranar asabar a Delhi bayan da aka sace wata yarinya mai shekaru 5 da haihuwa aka kuma ta yi mata fyede har tsawon kwanaki biyu.

An dai kama wani tumun da ake zargi da aikata hakan. Likitocin dake kula da yarinyar wadda ke bukatar ai mata babbar tiyata ko kuma fashi sun ce ta na sume.