An kammala zaben kananan hukumomin a Ivory Coast

Shugaba Alassane Ouattara
Image caption Zaben kananan hukumomin na tafiya lamin lafiya

An rufe rumfunan zabe a Ivory Coast bayan kammala zaben kananan hukumomin da aka yi shi cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da fargabar da aka yi ta yi a lokacin yakin neman zaben.

Jama'a dai ba su fito sosai don yin zaben ba, wanda jam'iyyar tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo ta kauracewa.

Hakan dai ya baiwa masu kada kuri'a zabi tsakanin jam'iyyu biyun da suka kafa gwamnatin hadaka.

Zaben shugaban kasar da aka yi a shekara ta 2010 wanda aka yi ta takaddama akai, ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane dubu 3.

Karin bayani