An hallaka wani dan jarida a Somalia

Sintiri a birnin Mogadishu
Image caption Yanayin tsaro ya yi muni a birnin Mogadishu a 'yan makonnin nan

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba sun harbe har lahira wani dan jarida da ke aiki a gidan talabijin din gwamnati dake Mogadishu, babban birnin Somalia.

Wasu mutane 3 ne suka kai wa Mohammed Ibrahim Rage hari lokacin da ya ke zaune a kofar gidansa bayan ya tashi daga aiki.

Watanni hudun da suka wuce ne ya koma Somalia, bayan ya kwashe shekaru yana karatu a Uganda.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kuma tun da Mr Rage na yiwa gidan talabijin din gwamnati aiki ne to ana nuna yatsa kan kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al-Shabaab, wadda ke fada da mahukuntan kasar.

Karin bayani