Sun yi yunkurin kai hari kan jirgin kasa a Toronto

'Yansanda a kasar Canada
Image caption 'Yansanda a kasar Canada

Ana tuhumar wasu 'yan kasashen waje biyu dake zaune a kasar Canada da yunkurin kai harin ta'addanci kan jirgin kasan fasinjoji.

An dai cafke mutanen biyu Chiheb Esseghaier da Raed Jase a ranar Litinin.

Ana zargin su ne da yunkurin gotar da jirgin a kusa Toronto, birni mafi girma na kasar Canada.

Mahukunta sun ce wannan ta'asa ka iya haddasa mutuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Jami'an tsaron Amurka na cikin masu gudanar da binciken da aka fara, tun lokacin da aka fara sa ido kan wadanda ake zargin a cikin watan Ogustan shekarar da ta gabata.

Mataimakin kwamishinan 'yansanda, James Malizia ya ce suna da shaidun da suka cewa wasu masu alaka da kungiyar al Qaeda a kasar Iran ne ke taimaka musu.

Ya ce abinda bincike ya nuna dai shine irin taimakon da suke samu ya jibanci saka su a hanya kan yadda za su kai harin.

Sai dai wasu rahotanni sun ce babu tabbacin cewa an yi yunkurin kai harin ne kan jirgin kasan dake kai komo tsakanin biranen Toronton kasar Canada, da kuma Newyork na Amurka.