Turawa da dama na agazawa 'yan tawayen Syria

Image caption Yan kasar Burtaniya da Faransa da kuma Ireland suka fi yawan turawan dake zuwa Syria yaki.

Shugaban Hukumar yaki da da ta'adanci na Kungiyar tarrayar Turai ya shaidawa BBC cewa daruruwan Turawa ne ke taya 'yan tawaye a Syria yaki da gwamnati Bashar al Assad.

Hukumomin leken asiri sun nuna damuwa cewa wasu daga cikinsu na iya shiga kungiyoyin kamar su Al-Qa'ida wanda daga baya kuma idan sun dawo Turai za su iya kaddamar da harin ta'adanci.

Shugaban Hukumar yaki da ta'adanci a Turai, Gilles de Kerchove ya yi gargadin cewa daruruwan Turawa ne ke Syria a yanzu a haka, inda yake cewa yawansu na iya kaiwa dari biyar.

Ya ce yawancinsu sun kaiwa 'yan tawaye dauki ne a Syria, amma akwai yiwuwar kungiyoyin ta'adda za su gurbata da dama daga cikinsu.

Alkaluma sun nuna cewa kasashen Burtaniya da Ireland da kuma Faransa ne suka fi yawan Turawan da ke taya 'yan tawaye yaki a Syria.

A kasar Burtaniya da Belguim hukumomin tsaro sun sa ido sosai su ga yadda ake cussawa wadannan Turawa ra'ayi zuwa yaki Syria.

Ita ma dai Kasar Holland ta tsaurara bincike musamman ga wadandake dawowa daga Syria saboda kada su dawo da tsau-tsauran ra'ayi.