Niger ta fada hannun James McComick

A yanzu haka dai ta tabbata cewa dan kasuwannan miloniya da aka samu da laifin sayar da na'urar gano bamabaman da aka binne a kasa na bogi ga kasar Iraki, ya sayar da irin wannan na'ura ga wasu kasahen Afrika da dama, da suka hada da jamhuriyar Nijar da kuma Kenya.

A jiya ne wata kotu a nan Birtaniya ta same shi da laifin aikata zamba.

Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta turo mana video na shaidar gwajin na'urorin da dan kasuwar ya yi ma sojojin Nijar.

Sai dai kuma gwamnatin Nijar din ta musanta yin wata cinikayya makamanciyar wannan.