Rashin aiki a Spain ya yi kamari

Matsalar rashin aikin yi a kasar Spain ta kai wata sabuwar makura. Sama da mutane miliyan shida---wato kashi ashirin da bakwai cikin dari--- na mutanan da ka iya yin aiki ne ba su da aiki.

Wannan shine kiyasin da akai a watanni hudun farko na wannan shekarar.

Masu aiko da rahotannin sun ce a bayyane ta ke cewa tattalin arzukun kasar Spain na kokarin fita daga matsalar da ya fada shekaru biyar din da suka wuce.

Mutane dai na kara nuna fushinsu game da matakan tsuke aljihun gwamnati, wadanda masu adawa da shi ke cewa yana ta'azzara matsalar.

Rahotanni daga Madrid sun ce 'yan sanda na cikin shirin ko ta kwana domin tunkarar gagarumar zanga zangar da aka shira yi nan gaba a yau a wajan majalisar dokokin kasar.