Amurka ta yi zargin yin amfani da makamai masu guba a Syria

Chuck Hagel, Sakataren tsaron Amurka
Image caption Chuck Hagel, Sakataren tsaron Amurka

Fadar shugaban Amurka ta ce ta na da shaidar cewa dakarun gwamnatin Syria sun yi amfani da makamai masu guba.

A wata wasika da ta aikewa majalisar dokokin Amurka, gwamnatin Obama ta ce hukumar leken asirin Amurka ta gudanar da bincike da abin da ta kira na tabbacin cewa an yi amfani da gubar sarin 'yar kadan.

Sakataran tsaron Amurka Chuck Hagel ya ce ba za mu iya tabbatar daga inda makamai masu gubar suka fito ba, amma mun yi ammanar duk duk wani makami mai guda da za'a amfani da shi a Syria gwamnati ce za ta yi.

To sai dai kuma Amurkar ta ce binciken na hukumar leken asirin kadai bai isa ya sauyawa mata matsayin a kan Syria ba kuma akwai bukatar MDD ta yi cikakken bincike dan tabbatar da gaskiyar lamarin.

Shugaba Obama ya ce amfani da makamai masu guba zai sa Amurka ta kara tsunduma cikin rikicin na Syria.

Karin bayani