Korea ta Arewa ta yi watsi da wa'adin tattaunawa

Kasar Korea ta arewa ta yi fatali da wa'adin da Korea ta kudu ta sanya mata na tattaunawa game da masana'antar hadin gwiwar kasashen biyu dake Gaesong.

Ayyuka sun tsaya cik a masana'atar dake yankin Korea ta Arewa makwanni uku da suka wuce.

Korea ta arewa dai ta hana ma'aikatan Korea ta kudu shiga masana'antar sannan kuma ta janye nata ma'aikatan.

Har yanzu dai akwai ma'aikatan Korea ta kudu da suke cikin ginin masana'antar su dari da saba'in da biyar.

Wa'adin da Korea ta kudu ta sanyawa arewa ya zo ne da gargadi.

Ta ce muddin Korea ta arewa bata amince da wa'adin zama teburin tattaunawa ba, toh za ta kuka da kanta.

Gwamnatin Korea ta kudu dai ba ta bayyana matakan da za ta dauka ba idan har Korea ta arewa ba ta amince da wa'adin da ta sanya mata ba.

Amma akwai bayanan dake nuni da cewa Korea ta kudu za ta janye ma'aikanta 175 dake masana'antar.

Toh haka kuma na iya nufin cewa Korea ta arewa za ta iya kwace kadarorin Korea ta arewa dake masana'antar kamar yadda ya faru a baya.

Ma'aikatan Korea ta kudu dai na fama da rashin abinci da magunguna kuma Korea ta arewa ta hana a shigo masu da agaji ta iyakar kasashen biyun.

Ma'aikatar hadin gwiwar dake Gaeson ta fuskanci kalubale da dama a 'yan shekarun da suka gabata kuma hakan na nuni da irin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Korea ta Kudu dai ta nemi a yi sulhu ne a yayinda ake zaman dar-dar tsakanin kasashen biyu a 'yan kwanakin da su gabata.