Ana kara gano mutane da rai a ginin da ya rufta a Bangladesh

Image caption Ana ci gaba da samun masu rai a buraguzan ginin

Ma'aikatan agajin gaggawa a Bangladesh sun zakulo karin mutnae ashirin da hudu wadanda suka tsira da ransu daga baraguzan ginin wasu masana'antun tufafi da ya rufta ranar Laraba.

Ma'aikatan sun kwashe daren jiya suna fafutukar ceto wasu mutanen da aka gano inda suke ranar Juma'a.

An hakikance cewa mutane fiye da dari uku sun rasa rayukansu, wadansu daruruwa kuma ba a san inda suke ba.

Mozharul Sakatare Janar na kungiyar ba da agaji ta Red Crescent a kasar ta Bangladesh.

Ya ce; "zuwa yanzu mun ceto mutane dubu biyu a raye amma da kananan raunuka, kuma rundunar sojin kasar ce ke jagorantar ayyukan ceto wadanda abin ya rutsa da su."

Masu masana'antu sarrafa kaya biyu dake ginin da ya rufta sun mika wuya ga 'yan sanda.

Mahbubur Rahman Tapas and Balzul Samad Adnan ana zarginsu ne da tursasawa ma'aikatansu aiki a ginin da ya rufta duk da gargadin da ake yi cewa ginin ya tsage.

Sama da mutane dubu uku ne ake ganin ke aiki a ginin a lokacin da ya rufta.

A ranar juma'a akalla mutane dubu goma ne suka fito zang-zanga inda suke kira ga gwamnatin kasar da ta kama mai ginin sannan kuma ta inganta yanayin rayuwar ma'aikantan da ke aiki a masana'antar sarrafa kaya a kasar.

Tuni dai mai gini ya boye a yayinda hukumomi a kasar ke nemansa ruwa a jallo.

Karin bayani