Mali: Faransa ta nemi Chadi ta bar dakarunta

Image caption Jean-Yves Le Drian, ministan tsaron Faransa

Minisitan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian ya buƙaci Chadi ta bar dakarunta su ci gaba da kasancewa a Mali domin kaucewa abinda ya kira yiwuwar samun giɓi.

Ministan tsaron na Faransa wanda ya ziyarci Chadi yace, yana tattaunawa da shugaba Idris Deby akan yadda dakarun Chadi zasu kasance cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya da zata yi aiki a Chadi.

Ranar Alhamis ne majalisar dinkin duniya ta amince da kafa wata rundunar kiyaye zaman lafiya da za'a aike zuwa Mali.

Kwanakin baya ne dai majalisar dokokin Chadi ta amince da soma janye dakarun kasar daga Chadi.