Adawa da rage ma'aikatan gwamnati a Girka

Masu zanga-zanga a Girka
Image caption Masu zanga-zanga a Girka

Masu zanga- zanga a Girka na ta taruwa a gaban majalisar dokokin kasar yayin da take shirin kada kuri'a kan wata sabuwar doka wadda za ta sa ma'aikatan gwamnati dubu 15 rasa ayyukansu nan da karshen shekara mai zuwa.

Dokar za ta maye gurbin wadda ke cikin kundin tsarin mulkin kasar da ta ba ma'aikatan gwamnati tabbacin aiki na iya tsawon rayuwa.

Rage ma'aikata na daga cikin sharrudan da aka shimfidawa kasar ta Girka don ta samu tallafin ceto tattalin arzikinta.

Gwamnati dai ta ce dokar za ta kara kyautata yanayin aiki ta hanyar sallamar ma'aikatan da ba su da da'a kuma za a samawa matasa masu kwazo aiki, sai dai masu zanga- zangar sun ce babu abin da dokar za ta haifar, illa ta kara ta'azzara matsalar rashin aikin da da ma ta yi kamari a kasar.

Karin bayani