Ana san a kori magoya bayan Gaddafi

Wani gungun mutane kimanin 50 dauke da makamai sun yiwa ma'aikatar harkokin wajan Libya dake Tripoli kawanya.

Wani da ya shaida lamarin ya ce akalla manyan motocin tarakta guda 30, wasunsu makare da bindigogi masu sarrafa kansu sun datse hanyar dake kaiwa ginin.

Masu zanga zangar na bukatar ma'aikatar ne ta kori mutanan da suka kira magoya bayan hambararrar shugaban kasar, marigayi Kanal Gaddafi.

Abdul Razak Al-Sarif, daya daga cikin mutanan da suka jagoranci datsewar ya ce suna san a yi dokar da zata kebe magoya bayan Kanal Gaddafin daga shiga siyasa a kasar, sabilida juyin juya halin da su kai tamkar an yi musu mana fashinsa ne ya koma karkashin magoya bayan tsohon shugaban kasar.