Gwamnatin Nijar ta ce za ta duba bukatun matasan Diffa

Shugaban Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaban Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou

Hukumomin Jumhuriyar Nijar sun amince da su gaggauta duba matakan daukar matasan jahar Diffa dake Gabashin kasar, aiki a kamfanonin hakar man fetur da ke yankin.

Gwamnatin kasar ta ce nan da 'yan kwanaki wakilanta da na matasan da shugabannin jahar za su yi wata ganawa tare da kamfanonin da ke aiki a yankin na Agadem a kan wannan batu.

Haka nan kuma gwamnatin ta ce za ta gudanar da wasu ayyukan kyautata jin dadin rayuwar jama'a a yankin.

Hukumomin Nijar din sun dauki wadannan matakan ne dai, a karshen wani taro da Firayim ministan kasar, Malam Briji Rafini, ya yi da matasan da shugabannin jahar ta Diffa a ranar Lahadi, a wani mataki na shawo boren da matasan ke yi a 'yan kwanakin nan.

A jiya ma sai da matasan suka yi dauki ba dadi da jami'an tsaro a garin Diffa, bayan wata zanga-zanga da matasan suka yi, saboda matsalar rashin aikin yi da suka ce ta addabe su.

Matasan wadanda suka lalata dukiyoyi masu yawa a lokacin zanga- zangar, na zargin hukumomi ne da mayar da su saniyar ware wajen daukan aiki a cibiyar hakar man fetur ta Agadem da ke yankin.

Yanzu dai kura ta lafa a garin na Diffa, amma matasan sun yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta cika alkawarukan da ta dauka ba, to za su sake fitowa kan tituna domin yin wata sabuwar zanga-zangar.

Karin bayani