Bangladesh: an fidda da ceto wasu da rai

Image caption Masu aikin ceto

An fara fidda tsammanin samun wasu daga cikin ɗaruruwan mutanen da gini ya rufta da su a Bangladesh da sauran numfashi, yayin da aka ceto gawarwakin mutane fiye da dari uku da saba'in ya zuwa yanzu.

Ma'aikatan agaji dake binciken ɓaraguzan ginin da suka shiga kwana na shida a yau suna amfani da manyan nau'rori domin ɗauke kankare.

Tun da farko Firaministar kasar Sheikh Hasina ta ziyarci wurin inda ta gana da iyalan da lamarin ya shafa.

Ta yi alkawarin cewa za'a kula da ma'aikatan da suka sami rauni.

Framinista, Sheikh Hasina ta kuma ce, babu wanda zai rasa aikinsa, kuma dukkansu za'a sake ɗaukarsu aiki a wasu masana'antu.