An gano halittun cutar zazzabin cizon sauro da ba sa jin magani

Image caption An gano halittun kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro da ba sa jin magani

Masana kimiya sun gano wata halittar da ke jawo zazzabin cizon sauro wadda bata jin magani.

Masu binciken sun samo halittun a yammacin Kasar Cambodia wadanda suke da bambanci da sauran halittun a kasashen duniya.

Wadannan halittun sun sami damar jurewa maganin artemisinin daga waraka- maganin da aka fi amfani da shi wajan yakar cutar zazzabin cizon sauro.

Rahotannin kin jin magani a yankin ya bayyana ne a shekara ta 2008.

Matsalar kuma tuni ta watsu zuwa sauran yankin Kudu maso Gabashin Asia.

Masanan sun bayyana Yammacin Camboia a matsayin wurin da aka fi samun kin jin maganin cutar zazzabin cizon sauro.

Yanzu masana kimiyyar na damuwa saboda kin jin maganin artemisinin din da halittar kwayoyin cutar zazzabin cizon sauron ke yaduwa.

Wannan maganin dai ana amfani da shi kusan a fadin duniya kan maganin zazzabin cizon sauro.

Maganin dai yana warkar da cutar a 'yan kwanaki kadan yayin da aka yi amfani da shi da wasu magungunan.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ya zama wajibi a hana yaduwar kin jin maganin da halittar kwayoyin zazzabin cizon sauro ke yi.

Karin bayani