Gwamnatin Niger ta soke ma'aikata da aka dauka a Agadem

Mamadou Issoufou
Image caption Mamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar gwamnati ta bada sanarwar rusa matakan da aka dauka na daukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba a fannin aikin hakar mai a yankin Agadem.

Hakan ya biyo bayan kafa wani kwamiti ne da Praministan Briji Rafini ya yi, wanda zai yi nazari a kan alkawuran da gwamnati ta dauka da nufin tunkarar wasu matsaloli masu nasaba da rashin aikin yi tsakankanin matasa, ba kawai a jihar Diffa ba, har ma da sauran wuraren da ake hakar ma'adinai.

A karshen makon nan ne matasa a jihar Diffa suka yi kone kone yayin wata zanga zanga kan rashin aikin yi.