Ringim: An hallaka mutane biyar

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Ringim, a jihar Jigawa Nijeriya na cewa mutane aƙalla biyar ne suka mutu sakamakon wasu hare hare da wasu 'yan bindiga suka kai a garin.

Maharan sun kai farmaki ne jiya da dare a kan ofishin 'yan sanda, da kuma wani banki.

Jihar Jigawa dai na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ba a cika samun irin wadannan hare-hare ba, tun bayan fara takun-saka tsakanin jami'an tsaro da wadanda ake zargi 'yan ƙungiyar da aka fi sani da Boko Haram.

Koda a makon da ta gabata dai 'yan bindiga da ake zargin 'yan ƙungiyar Boko Haram ne sun yi artabu da jami'an tsaro a Gashua dake jihar Yobe.